Wannan meat filling ne multipurpose, wanda za a iya yin shi domin samosa, springrolls, ko meatpie, ko meat bag, ko dai duk wani abu da mutum ya yi ra’ayin saka nama a ciki. Idan kin so har a alala ma kina iya saka shi, ko ki yi sauce da shi. Yana da matukar dadi da saukin yi.
Abubuwan bukata
1- 1kg mince meat
2- 1/4 cup vegetable oil
3- 2 tablespoons maggi powder
4- 1 teaspoon salt
5- 1 tablespoon mixed spices
6- 1 teaspoon curry powder
7- 1 onion
8- 2 tablespoons pepper mix
9- 1 tablespoon dark soy sauce
10- 2 carrots
11- 1 green pepper
12 – 2 tablespoons flour mixed with 2 tablespoons of water (make a flour paste)
Yadda ake yi
1- Ki zuba mai a cikin non stick frying pan. Idan ya yi zafi sai ki zuba mince meat. Idan kuma naman ba minced one ba ne to ki saka a cikin food processor ki nika shi.

2- Sai ki zuba kayan kamshi da dandano.

3- ki zuba curry
4- Sai ki zuba albasa

5- ki rufe ki bar shi da kanshi zai kawo ruwa. Sai bayan kamar minti goma ki bude.

6- ki zuba jajjagen tarugu, tattasai, da kuma albasa.

7- Ki saka dark soy sauce amma ba dole ba ne. Tana dai kara wa naman kamshi da dandano mai dadi.

8- ki zuba carrots da green pepper wanda kika yanka dice.

9- ki kawo wannan flour paste ki zuba (amfaninsa shi ne zai saka wannan filling ya zama juicy. Ba zai yi dakas ba cikinsa.)

10- Ga shi nan ya kammala.

Duk kyawawan nau’ukan kayan kitchen din da nake amfani da su za ku same su a Bakandamiya Shopping. Ku garzaya ku samu garabasa.