Miyar kuka tana daya daga cikin miyoyin gargajiyar Hausawa tun iyaye da kakanni. Ana samun garin kuka daga iccen kuka wanda wannan ganye nata ne ake busarwa a daka shi ya zama gari a yi miya da shi. Yana da muhimmanci ga jiki da lafiya. Daga cikinsu akwai; saukin narkewar abinci wato digestion. Kuka tana dauke da Vitamins da kuma Minerals. Tana saita jikin mutum, idan mai kiba ne ta daidaita masa jikinsa, haka idan mai tumbi ne zai koma daidai da jikinsa. Miyar kuka tana gyara fata. Kuka na daidaita suga na jikin mutum. Da sauransu.
Abubuwan bukata
1- 3 daddawa
2- 1 onion
3- dunkulen garlic 1
4- Attarugu 5
5- 1/4 cup manja
6- 2 tablespoons vegetable oil
7- 4-6 cups water
8- 8 pieces cooked lamb meat
9- 4 maggi cubes
10- 1/2 teaspoon salt
11- 2 tablespoons garin kuka.
Yadda ake yi
1- ki hada albasa, tarugu, tafarnuwa, da kuma daddawa a wuri guda ki jajjaga su.

2- ki dora stainless tower pots a tukunya sai ki zuba manja da mangyada. Idan sun yi zafi sai ki zuba wannan kayan miyar da kika jajjaga.

3- Ki zuba dafaffen namanki a ciki, ki saka seasoning sai ruwa (amma ruwan ya danganta da yawan da kike son miyar).

4- Sai ki zuba kukarki mai kyau ki kada da stainless whisk saboda kada ta yi gudaji.

5- Kun ga yadda ta yi bayan an gama. Minti uku kawai ta kara na sauke.

6- Na yi serving da tuwon masara. Za ku iya ci da semo, tuwon shinkafa, alkama da sauransu.

Muna da original tower pots a Bakandamiya Shopping. Muna da whisks na karfe da silicon. Akwai nau’ukan kayan kitchen masu kyau da nagarta.