Milo lava float wani desert ne wanda ake yi da milo, madara, ice cream da sauransu. Yana da dadi sannan yana da saukin yi. Kananan yara za su fi jin dadinsa. Idan kika iya yin shi kin huta sayen wasu kayan kwalama din.
Abubuwan bukata
1- 1 sachet milo
2- 2 tablespoons liquid milk
3- 2 scoops chocolate ice cream (you can use vanilla ice cream)
4- 1 cup fresh milk
5- 1/2 cup ice blocks
6- 1 tablespoon condensed milk
Yadda ake yi
1- Ki zuba condensed milk, liquid milk, da kuma milo a cikin glass cup.

2- Ki yi amfani da whisk ko kuma hand mixer ki motsa shi sosai.

3- A wani serving glass cup din daban, ki zuba kankara

4- Sai ki kawo fresh milk ki zuba a kan kankarar.

5- Sai ki zuba 2 scoops na ice cream

6- Sai ki dauko wannan hadin na milo wanda kika fara yi, ki zuba a kai.

7- Ana shan shi ne a lokacin da aka yi.

Za ku samu glass cups da nau’uka daban-daban na kayan kitchen a Bakandamiya Shopping.