Duk da cewa idan aka ce meatpie kowa ya san irin wanda ake nufi. Amma wannan da na zo da shi wani iri ne daban wanda aka yi twisting dinsa ya canja daga irin normal meatpie da kowa ya sani. Ku biyo ni ku ga yadda ake yin shi har kala biyu.
Abubuwan bukata
1- 4 cups flour
2- 1 teaspoon sugar
3- 1 teaspoon baking powder
4- 200g butter
5- 3/4 cup buttermilk (or yoghurt)
6- MULTI-PURPOSE MEAT FILLING
7- 2 eggs
Yadda ake yi
1- Ki zuba flour a babban bowl mai tsafta. Sai ki zuba sugar, baking powder, kwai guda daya (out of the 2), butter, sai buttermilk ko kuma yoghurt.

2- Bayan kin zuba duk kayan hadin sai ki yi ta motsawa har sai ya dunkule (babu bukatar karin ruwa. Idan kuma kin ga bai yi ba sai ki dan yayyafa kadan). Daga nan sai ki nannade a leda ki saka cikin fridge ya yi tsawon awa daya.

3- Ga shi nan bayan an ciro shi daga fridge. Ki dora a kan wood chopping board. Sai ki yanki kadan.

4- za ki yi flattening dinsa da fadi. Gwargwadon girman baking dish din da za ki amfani da shi.

5- ki yi greasing baking dish dinki.

6- ki dauki wannan dough wanda kika yi flattening ki saka a cikin dish din, then ki dauko filling ki zuba a ciki.

7- Sai ki sake yankar flour ki flattening ki yanka shi strips. Ki dauka ki jera su ta tsaye. Idan kin gama da wannan sai ki jera shi ta gicce amma wani a kan wani kamar dai yadda yake a jikin hoto. Then ki sa kitchen scissors ki saita bakin ki yanke.

8- Sai ki egg wash da cikon egg din nan guda daya. Ma’ana ki shafa a kai da silicon brush. Ki saka a pre heated oven ki gasa.

9- Shi kuma wannan za ki yayyanka flour din ne kanana. Sai ki saka hannu ki taba shi sai ya yi fadi kamar haka.

10- Na yi amfani da abun cikin deep fryer ne. Idan ba ki da ita ki garzaya a Bakandamiya Shopping. Ko kuma ki amfani da wani abu da kike da shi amma mai design. Za ki dora a kai ki danna a hankali. Sai ki zuba filling din a tsakiya. Then ki dago shi a hankali ki matse.

11- ki jera a kan baking tray sannan shi ma ki yi masa egg wash ki saka a oven ki gasa wutar sama da kasa amma a low temperature. Da ya yi minti goma zuwa sha biyar sai ki duba idan ya gasu ki cire.

12- ga shi nan bayan sun gasu. Sai a yi serving.
