Ku duba yadda ake avocado smoothie cikin steps biyu kacal. A wannan recipe kayan hadi guda hudu ne kawai ake bukata.
Abubuwan hadawa
- Avocado daya
- Madarar gari cokali uku
- Suga cokali biyu
- Vanilla flavour kadan
Yadda ake hadawa
- ki samu avocado ki bare bawon sa ki zuba flesh in a blender, ki sa madarar gari, sugar da ruwa kadan.
- ki yi blending dinsu. ki sa a fridge in ya yi sanyi sai asha.
Karin bayani
- Idan madarar ruwa za ki yi amfani da shi ba sai kinsa ruwa ba gun blending din.
- Avocado smoothie yana da dadi sosai ga amfani a jiki.