Uwargida ki shirya tsaf dan ganin wani salon sarrafa nikakken nama da kwai, wannan salon na da saukin yi ga masu gidan da ke fitar sassafe. Amare fatan za a gwada yiwa Angwaye da Abokanansu.
Abubuwan bukata;
1 -Kwai
2 -Flour
3 -Nikakken nama
4 -Kayan dandano
5 -Mai
6 -Kayan kamshi
Yadda ake hadawa;
- Farko ki hada nikakken namanki, idan ba ki da nikakken ki daka namanki ko ki yi blending dinsa, sai ki daura shi akan wuta kisa kayan kamshi da dandano ya tsotse sai ki ajiye a gefe.
- Shi kuma dafaffen kwan naki ki tsaga shi ta tsaye ki cire kwaiduwan ciki ki ajiye su a gefe.
- Sai ki dauko flour kisa kayan qamshi da dandano kisa ruwa kida mata da kauri.
- Daga bisa ni ki daura mai ya yi zafi akan wuta.
- Sai ki dauko kwai da kika cire cikinsa kisa namanki a ciki da kika hada, sai ki dauko daya barin kwan ki rufe dashi, ma’ana wannan naman shi kika sa a wurin kwaiduwan kwan da kika cire.
- Sai ki tsoma a hadin flour da ya kame jikinsa ko’ina ya ji, sai ki saka a cikin mai ya soye, haka za ki yi tayi har ki gama. Sai a yi serving.