Skip to content

Liver and kidney sauce

Share
liver and kidney sauce 1
1
(1)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Wannan Liver and kidney sauce din sauce ce wadda za a iya cin ta da komai, tun daga kan shinkafa, pasta, moimoi, wake, da sauransu. Ita kadai ma ana iya cin ta kuma a koshi. Tana da saukin yi sannan tana da dadi sosai. Tana da saurin cika ciki kamar yadda aka sani hanta na daya daga cikin protein din da za ka ci ta rike maka ciki ka jima ba ka ji yunwa ba.

Abubuwan bukata:

1- 1/2 cup liver

2- 1/2 cup kidney

3- 1/2 cup pepper mix (tattasai, tarugu, albasa)

4- 1 albasa mai lawashi

5- 1 tablespoon mixed spices

6- 1 tablespoon maggi powder

7- 1/2 cup vegetable oil

8- 2 tablespoons cornflour (optional)

9- water as required

10- 1 teaspoon curry

Yadda ake yi:

1- ki zuba mai a cikin non stick pan, sai ki zuba wankakkun hanta da kodar da za ki amfani da su.

liver and kidney sauce 2

2- Sai ki hada spices dinki wanda kike da su (na yi amfani da paprika, thyme, rosemary, garlic, ginger, black pepper) then maggi ki zuba duka a ciki

liver and kidney sauce 3

3- Sai ki saka curry

liver and kidney sauce 4

4- then ki saka albasa

liver and kidney sauce 5

5- Sai ki motsa su su hade sannan ki rufe ba sai kin zuba ruwa ba da kansu za su kawo ruwa.

liver and kidney sauce 6

6- bayan kamar minti shida sai ki bude ki zuba kayan miyar da kika jajjaga. Ki kara rufewa ya soyu na minti biyar.

liver and kidney sauce 7

7- Daga nan ki zuba ruwa makimanci sai ki bari ta karasa dahuwa.

liver and kidney sauce 8

8- idan kin tabbata komai ya dahu sai ki dama cornflour ki zuba a ciki saboda ta yi thick. Amma idan ba ki so da kaurin ma kina iya barin ta a hakan ba dole ba ne.

liver and kidney sauce 9

9- Bayan kamar minti uku za ki ga ta yi kauri

liver and kidney sauce 10

10- Shi ke nan sai ki sauke. Ki ci Liver and kidney sauce dinki da abin da kike so.

How many stars will you give this recipe?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page