Mu koyi yadda ake lemun kukumba da citta danya. Wannan lemun yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.
Abubuwan hadawa
- Kukumba (3)
- Citta (4)
- Suga
- Lemun tsami (5)
Yanda ake hadawa
- Da farko zaki sami kukumbarki ki wanke ki yanka kisa a blender.
- Sai ki wanke cittarki ki goga da abin goga kubewa ko ki yanka kisa a blender ki hada da kukumba ki markada.
- Sannan sai ki tace ki sa suga da lemun tsami.
- Daga karshe, sai ki sa a firinji ko kisa kankara.