Wannan lemo ne mai saukin yi, mai saukin kashe kudi, sannan mai dadi. Ni na kirkire shi da kaina na gwada kuma ya yi mini dadi, sannan ya yi wa family dina ma dadi.
Abubuwan bukata
1- 1 whole watermelon
2- 1/2 pineapple
3- 1/2 bottle sprite
4- Fresh flavor (watermelon flavor)
5- ice blocks
Yadda ake yi:
1- Ki yanka kankana kanana ki zuba a cikin blender mai kyau

2- Sai ki zuba abarba ma

3- Ki zuba ruwa kadan a ciki ki markada

4- Sai ki tace.

5- Ki zuba wannan fresh din na kankana.

6- Sai na juye shi a cikin kwallon kankanar da na bude na mayar da ita kofi. Ki zuba sprite a ciki.

7- Shi ke nan an gama. Ki zuba kankara a ciki.
