Skip to content

Kunun waken suya da alkama

Share |
kunun waken suya da alkama
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ga yadda ake kunun waken suya da alkama, mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai saukin bi ga kuma dadi. Cikin ‘yan lokaci kalilan uwargida za ki hada.

Abubuwan hadawa

  1. Alkama kofi hudu
  2. Waken suya kofi hudu
  3. Citta da kanunfari (Yanda zai miki amma ba dayawa ba)
  4. Madarar gari
  5. Suga

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki sami waken suya da alkamanki ki gyara ki cire dattin ciki (amma kowanne a kwano daban ko tray zaki gyara). Bayan kin gyara, sai ki daura non stick pan naki akan wuta kisa waken suya ki soya sama sama (kamar yanda ake soya gyada tayin kunun gyada).
  2. Idan waken suyanki ya yi za kiji ya fara kamshi. Sai ki cire ki bushe ki hada ta da alkama da kayan kamshi ki bayar a niko miki, bayan an kawo ki tankade ki sa a abu mai murfi wadda iska baya iya shiga (airtight container).
  3. Ki daura ruwa kadan a kan wuta idan ya tafasa sai ki dauko garinki ki deba kofi daya ki dama kamar yadda ake dama talge, sai ki zuba cikin ruwan kan wuta ki na juyawa kamar yanda ake talge.
  4. Idan ya yi kaurin da ki ke bukata sai ki sauke ki sa a dan kwano mai zurfi (bowl) ko kofi ki sa madara da suga ki juya. Daganan komai ya kammala, sai sha kawai! A sha dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Kunun waken suya da alkama”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×