Ga yadda ake jallof rice da dankalin turawa, mu koya ‘yanuwa. Wannan hadadden jollof rice ne mai rai da lafiya, uwargida kar ki bari a barki a baya.
Abubuwan hadawa
- Shinkafa tafasashshe (perboiled rice)
- Tarugu
- Tattasai
- Dankalin turawa
- Alaiyaho
- Albasa
- Maggi
- Kayan kamshi (grain citta da curry)
- Man gyada
Yadda ake hadawa
- Da farko ki gyara kayan miyanki (tarugu da albasa da tattasai) ki wanke, ki markada su tare gu daya, ki ajiye a gefe.
- Sai ki dauko dankalin turawa ki fere bawon ki wanke ki yanyanka su kanana (into cubes) sai ki tsane shi ki ajiye a gefe.
- Sai ki gyara ganyen alaiyahoki ki cire shi a jikin sandar sa ki wanke ki ajiye ba tare da kin yanka ba, albasa itama ki yanka ta, ajiye a gefe.
- Sai ki dauko tukunya ki daura akan wuta ki sa man gyada ki sa albasa ki soya sam a sama, sai ki kawo markaden kayanki ki sa a ciki ki soya sam a sam a.
- Daga nan sai ki dauko kayan kamshi ki sa, maggi ki sa (iya dandanon da zai miki), sai gishiri kadan ki sa a ciki ki juya sai ki kara ruwa kadan (dai dai wanda zai dafa miki shinkafa ba tare da ta cabe ba) sai ki Rufe tukunya ki na dan wani lokacin har sai kin ji ya fara tafasa sai ki dauko wani kwano daban ki raba ruwan vida biyu.
- Dauko tafasashshe shinkafanki tare da dankalin turawa ki na diba da mara (amfanin mara shine shinkafan bazai cabe ko ta karkarye ba) ki na zubawa ki na yaryada Dankalin turawa akan shinkafan kina kuma xuba ruwan hadinki akai, haka za ki yi har ki gama da shinkafa da dankalin turawan, bayan kin gama sai ki sa mara ki juya ta a hankali harsai sun hade juna.
- Sai ki rufe saman shinkafarki da leda ko foil paper ( ta yadda tiririn bazai na fitawa ba) sai ki kawo marfin tukunya ki rufe nadan wani lokaci har sai kinji ruwan ya shanye sai ki dauko alaiyahonki ki sa a ciki ki juya ki sake rufewa ki kashe wutanki nadan wani lokaci. A ci dado lafiya.