Da yawa wasu sun dauka dole sai dai su fitar da kudi su je shago su sayi ice cream, wai ba za su iya yi a gida ba. Idan kina daga cikin masu irin wannan tunanin, to tsaya ki kalli yadda na hada wannan ice cream din a cikin gida, tare da popsicle mai dadi.
Abubuwan bukata:
1- 1 cup whipping cream
2- 1/2 cup cold water
3- 1 cup heavy cream
4- 1/2 cup condensed milk
5- 1/2 teaspoon vanilla flavor
Yadda ake yi:
1- Ga abubuwan bukata

2- Ki zuba whipping cream da ruwan sanyi a bowl ki mixing sosai har sai ya zama whipped. Sai ki zuba heavy cream da condensed milk.

3- sai ki saka flavor ki mixing da kyau.

4- Ga yadda kwabin zai zama nan.

5- Sai ki dauko popsicle mould dinki ki soka sticks a jiki sannan ki zuba abin da kika hada din. Ki nade da cling film. Ragowar ma ki nade da cling film sai ki saka a freezer overnight

6- Ga shi nan bayan gari ya waye ya zama kankara duka

7- Sai ki cire a hankali daga jikin mould din. Daga nan sai na yi drizzling chocolate a kai.

8- Na yi scooping ice crdam din a cikin kyakkyawan cup sai ki yi drizzling chocolate. Then ki mutmusa oreos da lotus biscuits

9- Sai ki serving. Wannan ice cream din ne.

10- wannan kuma popsicle din ne.
