Skip to content

How to prepare gas meat

Gas meat 1
4
(3)

Akwai hanyoyi da dama na sarrafa nama, gas meat yana daga ciki. Yana da saukin yi, sannan yana da dadi. Za a iya amfani da naman sa ko na rago. Ku biyo ni domin ganin yadda na sarrafa nawa.

Abubuwan bukata:

1- 1/2kg naman rago

2- 1/2 cup kuli kuli powder

3- 1 sachet beef seasoning

4- 3 seasoning cubes (maggi, mr chef, onga)

5- 5 garlic

6- 2 large onions

7- 3 scotch bonnets

8- 1/2 sachet nutmeg

9- 1/4 cup vegetable oil

Yadda ake yi:

1- ki wanke nama ki yanka shi da fadi kamar yadda na yi

Gas meat 2

2- sai ki zuba a cikin sauce pan ki dora kan wuta. Ki zuba 1/3 na albasarki.

Gas meat 3

3- Ki zuba dandano yanda zai ji.

Gas meat 4

4- sai  ki zuba beef seasoning da nutmeg

Gas meat 5

5- Ki zuba garlic da kika jajjaga.

Gas meat 6

6- Sai ki bari ya dan fitar da ruwa sannan ki kara wani ba mai yawa sosai ba.

Ga meat 7

7- Idan naman ya dahu sosai sai ki zuba ragowar albasar.

Gas meat 8

8- Ki zuba garin kuli kuli da attarugu ko kuma dakakken yaji.

Gas meat 9

9- Ki zuba mai.

Gas meat 10

10- sai ki jujjuya shi ya hade.

Gas meat 11

11- idan ya yi kamar minti biyar a low heat sai ki sauke

Gas meat 12

12- Sai ki yi serving da waina ko sinasir ko kuma duk abin da kike so.

Gas meat 13

Ku shiga Bakandamiya shopping domin samun kayan kitchen a cikin rangwame da rahusa.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×