Ga wani honey citrus hibiscus iced tea mai matukar dadi sannan yana da saukin yi. Idan kina da hibiscus tea bag za ki iya amfani da shi a wannan recipe din, ya fi sauki.
Abubuwan bukata
1- 1/2 cup Active Citrus Juice
2- 20ml lemon juice
3- 3 pieces zobo
4- 1/2 cup hot water
5- 1/2 cup ice blocks
6- 1 tablespoon pure honey
Yadda ake yi
1- Ki dauki zobo guda uku ki zuba a cikin cup. Sai ki zuba ruwa mai zafi wanda ya tafasa.

2- Ki rufe ki bar shi ya jika na akalla minti biyar.

3- Daga nan ki dauko serving glass cup dinki ki zuba active chivita na citrus.

4- Sai ki zuba lemon juice a ciki.

5- Ki zuba zuma

6- Sai ki zuba kankara a ciki mai dan yawa. Ita za ta kusan cika cup din

7- Daga nan sai ki kawo wannan zobon da ya jika ki karasa cika cup din da shi.

8- Shi ke nan sai ki yi serving.
