Idan ke ma’abociyar shan zaki ce musamman chocolate, ko kuma kina yin business wanda ya danganci wani abu da za a yi filling ko topping da chocolate. To ya kamata ki tsaya ki duba yadda na hada wannan chocolate din a cikin gida, mai matukar dadi.
Abubuwan bukata:
1- 1 cup icing sugar
2- 1/2 cup cocoa powder
3- 1 and 1/4 cups powdered milk
4- 1 cup liquid milk
5- 1 tablespoon butter
Yadda ake yi:
1- Ga abubuwan bukata

2- Za ki zuba madara, da liquid milk a cikin sauce pan.

3- Sai icing sugar da cocoa powder

4- dai ki motsa da kyau. Wutar za ta zama medium low flame.

5- Bayan kamar minti biyar sai ki zuba butter

6- Sai ki kashe wutar ki juya da kyau. Idan kin ga akwai lumps sai ki tace.
