Komai wanda za ka yi a gida ya fi dadi fiye da wanda za ka saya. To bread ma yana daga cikin abubuwan da in dai ka gwada yin su a gida ba za ka sake yarda ka saya a waje ba. Baya ga haka, ya yi tsada yanzu. Hakan ne ya sa na yanke shawarar kawo maku yadda ake yin bread a cikin gida. Wato homemade bread in ji turawa.
Abubuwan bukata:
1- 4 cups flour
2- 1 egg
3- 1/2 cup sugar
4- 1 tablespoon yeast
5- 3 tablespoons butter
6- 1 cup liquid milk
7- 1/2 teaspoon salt
Yadda ake yi:
1- ki zuba madara a cikin standing mixer. Madarar gari ce 1/4 cup na dama da ruwa 1 cup.

2- Sai ki fasa kwai a ciki

3- Ki zuba active yeast wanda bai sha iska ba

4- Sai ki zuba sugar. Daga nan za ki rufe ki bar shi na minti goma za ki gane yeast dinki mai kyau ne idan bubbles sun taso a sama.

5- Ga shi nan bayan minti goma

6- Sai ki zuba flour a ciki

7- ki zuba butter a ciki. Amma na fi son amfani da blueband a bread.

8- Ki zuba gishiri

9- Daga nan ki yi mixing a mixer na minti goma sha biyar. Idan ba ki da mixer za ki buga shi ne da hannu har sai kin ji babu nauyi kwata-kwata

10- Ga shi nan za ki gan shi soft dough kamar haka

11- Sai ki raba shi guda goma sha biyu

12- Sai ki mulmula shi da kyau kamar haka.

13- Sannan ki yi amfani da rolling pin ki murza shi ya dan yi fadi amma ba sosai ba

14- ki nannde shi kamar haka

15- Ki yi greasing baking dish dinki mai dan fadi sai ki yi arranging kamar yadda na yi.

16- Sai ki samu leda cling film ki nannade shi ki rufe har sai ya yi doubling size dinsa.
17- Ga shi nan ya yi doubling size din

18- Sai ki shafe saman da madara

19- Sai ki sa a pre heated oven ki gasa da wutar kasa kawai. Sai ya gasu ki kunna wutar sama.

20- Ga shi nan bayan ya gasu. Sai ki shafa butter a samansa

21- Ki lullube shi na minti goma. Hakan yana kara masa taushi sosai.

22- To ga shi nan bayan na bude. Idan kin kunna wutar sama kada ki yi nesa da shi. Ni ma wani uzurin ne na je yi shi ya sa ya dan fara konewa. Thank God bai kone sosai ba kuma na ji dadinsa a haka.
