Asalin shayi kalmar Larabci ce wanda Bahaushe ya ara. Shayi yana da matukar muhimmanci ga lafiyar dan’adam. Likitoci sun yi bincike sun gano cewa yana kawo kariya daga matsalar ciwon zuciya. Idan kuwa mutum yana fama da wannan ciwo na zuciya, to zai saukaka daga illolin da wannan cutar take haifarwa (Peter Kistler). Idan aka zo fagen shayi mai kayan yaji kuwa, yana maganin duk wani abu da ya danganci sanyi, tun daga kan asthma, pneumonia, da kuma mura. A yau na zo maku ne da tsarabar yadda za ku hada kayan shayinku mai kamshi sannan da karin lafiya.
Abubuwan bukata:

1- 1 teaspoon ginger powder
2- 1 teaspoon cloves
3- 2 star anise
4- 6 cardamom pods
5- 1/2 teaspoon black pepper
6- 1/4 teaspoon cinnamon powder
7- 1/2 cup dried mint leaves
8- 1/4 cup dried lemon grass
9- 1 lemon
10- 4 cups water
11- Sugar or honey to taste
12- 2 lipton
Yadda ake yi
1- Bayan kin hada wancan jerin spices kin nika su. Sai ki zuba 2 tablespoons a cikin borosilicate pot ko kuma tea kettle

2- Sai ki zuba ruwa a ciki

3- Sai ki saka lipton da dried ko kuma fresh lemon. Ko lemon juice ma.

4- Sai ki rufe ki bari ya tafasa.
5- Za ki bar shi ya tafasa sosai ne ba wai tafasa guda daya ba. Sai kin ji kamshinsa yana tashi sosai.

6- Daga nan sai ki tace ki zuba a cup

7- Ki zuba sugar ko kuma zuma yadda kike son zakin ya kasance.

8- Ki yi serving a cup and saucer

Akwai cup and saucer da teapots da wasu nau’uka na kayan kitchen a Bakandamiya Shopping.