Akwai hanyoyi da dama na sarrafa kaza, tun daga kan farfesu, jar suya, dambun kaza, da sauransu. Kazar Hausa na da matukar dadi fiye da ta Turawa, saboda ita babu sirkin wani chemical a cikin abincinta. Halastaccen abincin da zai inganta lafiyarta ne, don haka ta kasance kaza mafi dadi fiye da ta Turawa har kuwa ga lafiyar mu. Shi ya sa na zabi na koya muku yadda za ku gasa ta ta yi dadi.
Abubuwan bukata
1- Kaza guda daya (a gyara a wanke kada a yanka).
2- Citta da tafarnuwa 1 tablespoon
3- 2 bay leaves
4- 4 cardamom pods
5- 2 allspice seeds
6- 1/4 teaspoon sea salt
7- 1/2 teaspoon paprika
8- 1 teaspoon salt
9- 2 maggi star
10- 1 Mr chef
11- 1 spoonful scallions
12- 2 cups water
13- 1 tablespoon yaji
14- 2 tablespoons vegetable oil
Yadda Ake yi
1-ki wanke kaza da kyau, sai ki saka a tukunya.

2- ki zuba kayan kamshin da na lissafa duka a kan kazar.

3- ki zuba dandano ma a kai.
4- ki zuba albasa mai lawashi.
5- sai ki zuba ruwa ki rufe ta ta dahu na minti talatin (ba tubus za ta yi ba.

6- Ga kazarmu nan bayan minti talatin mun sauke. Ruwa ta tsotse a jikinta.

7- Ki hada dakakken yaji, mai, da ruwa dan kadan a wuri guda sai ki motsa ki ajiye a gefe.

8- Ki hada gawayinki a kan local griller idan kin so za ki iya yi a oven. Sai ki dora kazar ki bar ta ta gasu na minti ashirin (ya danganta da taurin kazar).
9- Bayan kin tabbatar ta gasu sai ki shafe ta sosai da wannan hadin yajin da kika yi. Za ki yi amfani da silicon brush saboda wuta ba ta yi masa komai. Ki tabbatar da ko’ina ya shiga da kyau.

10- To ga kazarmu nan bayan ta gasu. Yaya kike tunani idan kika tarbi mai gidanki da wannan kaza musamman a lokacin azumi?

Za ku samu kayan kitchen nau’uka daban-daban a Bakandamiya Shopping.