Faten wake abinci ne mai muhimmanci, yana da dadi, sannan yana da kyau a jiki. Da yawa suna yi wa marassa lafiya shi, musamman rashin lafiyar da ya shafi rashin wadatar protein ko kuna rashin jini. Na zo maku da hanya mai sauki ta yin shi.
Abubuwan bukata:
1- 3 cups wake
2- 1/2 kg ‘yan ciki
3- 1 handful alayyahu
4- 2 spring onions
5- 5 seasoning cubes
6- 1 teaspoon salt
7- 1 cup palm oil
Yadda ake yi:
1- ki tafasa ‘yan ciki da albasa da kayan kanshi da magi.

2- ki tafasa wake bayan ya dahu ki tsame shi a colander

3- Bayan ‘yan cikin sun dahu sai ki zuba manja a cikinsu.

4- idan manjan ya yi, sai ki zuba alayyahu, albasa, seasoning, da gishiri. Ki bari su yi minti bakwai zuwa goma.

5- Sai ki zuba waken a ciki ki motsa.

6- kada ki bari ruwa ya yi kadas. Idan ya kare ki zuba kadan ki dame waken. Ki tabbata ya yi tubus sannan ki sauke.

7- A yi serving a kyakkyawar warmer ko kuma Plate irin na Bakandamiya shopping.
