Egg sauce, ko in ce miyar kwai, miya ce instant, wacce za a iya yin ta a take kuma a ci ta a dan gajeren lokaci saboda saukin yin ta. Tana dauke da protein (kwai), da kuma vegetables (kayan miya) masu kara lafiya musamman protein da yake gina jikin mutum. Tana da dadi sosai, sannan za a iya serving dinta da duk abin da ake so (multi-purpose). Yaya kike tunani idan kika yi ta a cikin azumi?
Abubuwan bukata
1- 3 eggs
2- 2 tattasai
3- 4 tomatoes
4- 6 attarugu
5- 1 onion
6- 3 maggi cubes
7- 1 teaspoon spices of choice (na yi amfani da curry, ginger and garlic powder, black pepper, and all purpose)
8- 1/2 cup vegetable oil
9- 1/2 teaspoon salt (or to taste)
10- 1/2 tablespoon sugar (option)
Yadda ake yi
1- Ki zuba kayan miyar da na lissafa a sama. Sai ki nika a cikin active food processor

2- Kun ga yadda ya niku. Duk da a kankare yake amma hakan bai hana active food processor sarrafa shi yadda take so ba, a cikin seconds arba’in ko kasa da haka. Kuma ban saka ruwa ba.

3- Sai ki zuba mai a cikin pan, idan ya yi zafi ki juye wannan kayan miyar da kika nika.

4- Sai ki zuba dandano, spices, salt, and sugar.

5- ki rage wuta ki bari ta dahu. Idan ta dahun kuma ki bari a bude ta soyu na minti biyar. Idan za ki yi amfani da non stick frying pan kada ki yi amfani da tools din karfe don kada su gurje miki pan. Ki yi amfani da silicon tools, ko na rubber, ko kuma wood.

6- Bayan ta gama soyuwa ta fitar da mai, sai ki zuba egg din a ciki

7- Kada ki motsa tukunna har sai ya yi minti daya

8- To daga nan sai ki motsa.

9- Bayan minti daya zuwa biyu sai ki sauke. Shi ke nan ta dahu.
10- Za ki iya cin ta da komai kamar yadda na fada a baya.

Muna da kayan kitchen masu kyau da inganci a Bakandamiya Shopping.