Skip to content

Danwaken shinkafa da fulawa

Share |
yadda ake danwaken shinkafa da fulawa
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

A yau zamu koya muku dan waken shinkafa da fulawa, ku biyo min cikin shafin nan na Bakandamiya Kitchen dan ganin yadda za a sarrafa shinkafa ayi dan wake da ita.

Abubuwan hadawa

  1. Shinkafar tuwo
  2. Fulawa (flour)
  3. Kuka
  4. Kanwa
  5. Man gyada
  6. Maggi
  7. Yaji

Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki sami shinkafarki ta tuwo kiwanke ta fita tas
  2. Sai ki kawo ruwan duminki mai zafi sosai ki zuba akan wankekken shinkafarki ya dan yi kamar minti 20
  3. Bayan ya yi kamar minti 20, sai ki tsanyaye ruwan ki bayar a kai miki inji a markada. Kar a sa ruwa a yi shi da kauri
  4. Bayan an markada sai ki kawo fulawarki ki tankade a kan markadadden shinkafarki, sai ki saka kuka da ruwan kanwar da kika jika
  5. Sai ki kwaba sai yayi daidai kaurin da ki ke so
  6. Sannan sai ki fara sakawa a ruwan zafin da kika dora ya tafasa. Sai ki dinga jefawa idan yayi sai ki sauke ki kwashe ki tsane
  7. A saka mai da yaji da salad a ci da mai gida da yara

A ci dadi lafiya.

Photo Credit: Fancy’s Bakery

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×