Dambu abinci ne na gargajiya, ko in ce na Hausawa, wanda mafi rinjaye aka fi sanin shi ga mutanen Katsina. Ana yin dambu da shinkafa, masara, gero, acca, da sauran wasu nau’ukan na hatsi. Dambu yana da dadi musamman idan ya hadu da gwana a wurin sarrafa shi. Ya kuma samu wadataccen zogale, nasan kunsan amfanin zogale a jikin dan adam, bayan karin jini da yake yi, yana maganin cututtuka da yawa musamman ciwon sugar. Wannan dalilin ne ya sa a yau na zo maku da hanyar da za ku sarrafa shi da shinkafa. Da kalilan din kudi, sannan ga shi da auki. Da wannan measurement nawa za ku iya ciyar da mutum bakwai ko takwas su koshi.
Abubuwan bukata
1- Shinkafa 1/2 mudu
2- Busasshen zogala 1/2 mudu (or fresh)
3- 2 sachets ajino moto
4- 1 tablespoon salt
5- 1 cup vegetable oil
6- 1/4 cup water
7- 2 tablespoons groundnut (gyada marau)
8- 2 albasa mai lawashi.
Yadda Ake Yi
1- Ki tsince zogala ki wanke shi tas sannan ki jika shi idan busasshe ne. Idan kuna fresh ne ki wanke shi kawai bayan kin gyara.

2- Sai ki barza shinkafa ki wanke ta da kyau sannan ki tsane ta daga ruwa. Sai ki zuba a roba ki tsame zogalar ma ki zuba a cikin shinkafar.
3- ki motsa su da kyau

4- ki dauki steamer ki zuba ruwa a ciki sannan ki zuba wannan hadin shinkafa da zogalar.
5- Sai ki dora a wuta ki turara su na minti talatin.

6- Sai ki juye shi a roba, ki zuba farin magi da gishiri, albasa da gyada.

7- ki zuba mai sai ki yayyafa ruwa (ruwa yana taimaka wa dambu ya yi taushi sosai).
8- Sai ki sake mayarwa a cikin steamer ya turara na wasu minti talatin din.
9- Ki daka kuli-kulinki da dandano, barkono, gishiri da kuma kayan kamshi.

10- Daga nan sai ki sauke shi ke nan ya dahu. Na ci nawa da soyayyen mangyada da dafaffen kwai. Za ki iya ci a haka ko ba ki kara mai ba idan ke ba ma’abociyar son maiko ba ce.

Za ku samu steamer, da plates, da spoons, da wasu nau’ukan na kayan kitchen a Bakandamiya Shopping.