Skip to content

Dafaffiyar doya da miyar kwai

dafaffiyar doya da miyar kwai
5
(6)

Ku koyi yadda ake dafaffiyar doya da miyar kwai. Wannan hadin na da dadi da kuma sauki wajen hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.

Abubuwan hadawa

  1. Doya (gwargwadon bukata)
  2. Kwai 4
  3. Albasa 2
  4. Maggi 4
  5. Attarugu 3
  6. Kori
  7. Man girki
  8. Tafarnuwa 2
  9. Gishiri

Yanda akehadawa

  1. Da farko zaki fere doyarki ki wanke ki sa atukunya da dan gishiri
  2. Idan yayi sai ki sauke ki zuba a kwanonki
  3. Ki fasa kwanki ki jajjaga attarugu ki yanka albasarki
  4. Ki sa kaskonki a wuta kisa mai ya danyi zafi sai ki zuba kwai kisa attarugu, da albasa, da maggi, da tafarnuwa, da kori,
  5. Sai ki dinga juyawa kadan-kadan kar kisa wuta sosai
  6. Idaan yayi sai ki sauke ki kawo doyarki ki zuba

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×