Cow tail, wato bindin sa, yana da matukar dadi, don zan iya cewa ya zarce kai da kafa ma dadi. kusan duk wanda ya tashi sarrafa shi to farfesu ake yi. Shi ne yau na ce bari in gwada maku yadda za ku yi miyar ja da shi. Ta yi dadi kwarai. Sannan procedure din da na bi na yi wannan miyar, za ta iya fin sati guda ba tare da ta yi komai ba, ko da ba a cikin fridge ko freezer ba ne.
Abubuwan bukata
1- 1 Bindin sa guda
2- 3 maggi cubes
3- 1 tablespoon mixed spices
4- 2 cups vegetable oil
5- 1/2 custard bucket na kayan miya (tattasai, tarugu, tumatur)
6- 2 onions
7- 2 sachets tomato paste
8- 8 maggi cubes
9- 2 knor cubes
10- 1/2 tablespoon mixed spices
11- 1 teaspoon curry powder
12- 1/2 teaspoon salt
13- 1 dunkulen garlic
Yadda ake yi
1- ki tsaftace cow tail ki saka a cikin pressure pot. Ni nawa kankararre ne shi ya sa yake a dunkule.

2- Bayan ya dauko hanyar dahuwa, sai ki sauke ki zubar da ruwan ki sauya wani. Then ki zuba maggi da gishiri da spices.

3- ki juye kayan miyarki a cikin tukunya. Sai ki zuba garlic wadda kika bare.

4- sai ki zuba mai a ciki ki rufe ki bar shi ya dahu na tsawon minti ashirin a low flame.

5- Bayan ya dahu sai ki juye a cikin food processor, ki saka albasa.

6- Ki markada shi.

7- Sai ki juye a cikin wok pan ki rufe. Kada ki sa wuta da yawa.

8- Bayan ruwan ciki ya gama tsotsewa, sai ki zuba seasoning and spices, curry, tomato paste, and vegetable oil.

9- Idan ta soyu za ki ji kamshinta yana tashi sosai. Sai ki juye wannan cow tail din a ciki tare da ruwansa.

10- Sai ki yi dandano ki ji yanayin yadda dandanon ya yi, daga nan ki zuba gishiri to your own taste. Ki rufe ta karasa na minti goma.

11- Ga miyarmu nan bayan ta nuna.

12- Za ki ci da abin da kike so. Ni dai na yi serving da shi kafa da wake.

Ku shiga Bakandamiya Shopping domin samun kayatattun kayan kitchen.