Idan kina neman abu wanda yake sanyaya makoshi mai dandanon cakuleti, to kada ki wuce wannan recipe din. Yana da sauki sannan yana da dadi sosai.
Abubuwan bukata:
1- 1 and 1/2 cups powdered milk
2- 1 cup peak milk powder
3- 7 sachets chocolate cowbell milk
4- 2 liters water
5- 1/2 cup whipping cream
6- 1 tablespoon chocolate flavor
7- 1/2 cup sugar
8- 1/4 cup heavy cream
Yadda ake yi:
1- Ga abubuwan bukata.

2- Ki zuba peak milk a cikin waccan madarar garin, sai ki zuba sugar, whipping cream, da kuma heavy cream.

3- Ki zuba chocolate cowbell, ruwa lita biyu, sai flavor. Chocolate flavor ya kamata amma ba ni da shi sai na yi amfani da butterscotch.

4- Bayan kin motsa shi sai ki tace.

5- Sai ki serving a cikin kyakkyawan cup dinki. Ki shiga Bakandamiya shopping za ki samu kyawawan cups.

6- Sai na zuba wani a cikin bottles masu kyau da tsafta.
