Skip to content

Chocolate and vanilla cookies

Share
Chocolate and vanilla cookies 1
0
(0)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Cookies, ko in ce biscuits, wani nau’in snack ne mai saukin yi, sannan mai dadi. Yana iya daukar tsawon lokaci ba tare da ya lalace ba. Ku biyo ni domin ganin yadda na yi wannan mai taushi mai dadi.

Abubuwan bukata:

1- 3 and 1/2 cups flour

2- 1 cup sugar

3- 1/2 cup powdered milk

4- 1 sachet butter

5- 2 eggs

6- 1/3 cup Cocoa powder

7- 1/4 teaspoon baking powder

8- 1/2 teaspoon flavor

yadda ake yi:

1- Ga abubuwan bukata nan.

Chocolate and vanilla cookies 2

2- Ki zuba butter a cikin bowl, ki zuba sugar ki mixing har sai ya game sosai ya zama creamy. Sannan ki fasa kwai ki zuba shi ma ki yi mixing da kyau.

Chocolate and vanilla cookies 3

3- Sai ki zuba flavor, ki sa madarar gari ki mixing. Bayan ya hade sai ki zuba flour amma ba duka za ki juye ba, ki rage kamar rabin kofi.

Chocolate and vanilla cookies 4

4- Ki cire 1/3 na dough din a wani bowl daban. Sai ki zuba ragowar flour din a cikin wanda yake da yawan. Ki karasa mixing sannan ki nade a cikin cling film ki saka a fridge.

Chocolate and vanilla cookies 5

5- Wancan 1/3 din da kika cire za ki zuba cocoa powder da baking powder ki karasa motsawa. Then ki nade shi a cling film ki saka a fridge

Chocolate and vanilla cookies 6

6- Bayan minti sha biyar sai ki ciro shi daga fridge din.

Chocolate and vanilla cookies 7

7- ki murza mai chocolate din har sai ya yi dogo. Sannan ki flattening na white din. Ki dora chocolate din a kan white din then ki nada shi kamar kina nade tabarma.

Chocolate and vanilla cookies 8

8- ki sa fork ki zana saman. Sannan ki yanka shi size din da kike so. Daga nan Ki arranging a baking tray

Chocolate and vanilla cookies 9

9- Sai ki sa a pre heated oven ki gasa da wutan sama da kasa a medium heat na minti sha biyar.

Chocolate and vanilla cookies 10

10- Shi ke nan idan ya gasu sai ki cire. Za ki iya storing dinsa na kwanaki ba tare da ya yi komai ba.

Chocolate and vanilla cookies 11

Ku leka Bakandamiya shopping ku sayi zafafan kayan kitchen.

How many stars will you give this recipe?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×