Idan aka ce suya, kai tsaye abin da yake zowa a ran mutum shi ne tsire na naman sa ko kuma rago. To a yau na zo maku da wata hanyar daban wadda za ku yi tsire mai kuli amma da naman kaza. Shin ta yaya? Ku biyo ni ku ga yadda za a haihu a ragaya.
Abubuwan bukata:
1- kuli-kuli na 500
2- 1 maggi star and 1 onga cube
3- 1/2 teaspoon salt
4- 1 bunch garlic
5- 1 teaspoon spices of your choice
6- 2 large chicken breasts
7- 1/4 cup vegetable oil
8- 1 and 1/2 tablespoons yaji
9- 1 tablespoon sansamin yaji
10- 1 tablespoon maggi powder
11- 1 tablespoon mixed spices
Yadda ake yi:
1- Ki daka kuli ya zama gari sosai

2- Sai ki yanka naman kazar into cube, size din da kike so. Sai ki zuba yaji, magi, spices, da kuma rabin Manki. Ki murza sosai har sai komai ya game jikin kazar.

3- Sai ki zuba 3 tablespoons na garin kulin nan da kika daka. Ki sake murzawa sosai sai kulin nan ya shiga jikin naman.

4- Already kin jika skewers dinki. Amfanin hakan shi ne dan kar ta kone. Sai ki arranging wannan kazar a jikin skewers ko kuma tsinken tsire yadda kike so. Then ki kara barbada kulin a kai bayan kin gama.

5- Sai ki zuba mai a cikin grill pan, za ki iya yi a non stick frying pan, ko air fryer, ko ma a oven. Daga nan sai ki jera tsinkar naman a kai.

6- za ki dinga yi kina juyawa bayan kowanne minti biyar. Sannan wutar za ta zama medium. Duk kika juya sai kin barbada kuli kuli ki shafa mai.

7- A haka har sai kin tabbatar da naman nan ya gasu. Minti sha biyar zuwa ashirin da wuta kadan don kar ya kone.

8- Shi ke nan sai ki sauke ki yi serving.

Akwai kyawawan kayan kitchen a Bakandamiya shopping. Su grill pan, non stick frying pan, air fryer da sauransu.