Idan kina neman abu mai dadi da kashe kwalama, to aka ce muku chicken nuggets kankat ke nan. Yana da saukin yi da kuma dadi. Kananan yara za su so shi sosai musamman masu zuwa makaranta.
Abubuwan bukata:
1- 2 chicken breast
2- 1 cup all purpose flour
3- 1 teaspoon cornflour
4- 1 tablespoon spices of your choice
5- 1 egg
6- 1/2 cup liquid milk
7- 1/2 teaspoon curry
8- oil for frying
9- 1/2 teaspoon salt
10- 1 tablespoon maggi powder
Yadda ake yi:
1- Ki samu chicken breast ki wanke tas ki yanka shi cubes. Sai ki zuba seasoning da salt
2- Ki zuba spices. Na yi amfani da black pepper, paprika, chili flakes, ginger and garlic powder. Za ki iya amfani da wanda kike da shi

3- Then kwai

4- Bayan duk kin zuba a kan naman, sai ki zuba madara (ki dama madarar gari da ruwa)

5- Sai ki murtsuka su shiga ciki sosai. Then ki rufe ki bar shi na awa biyu ko uku

6- A wani bowl daban ki zuba flour, then ki zuba gishiri a kai
7- Ki zuba cornflour amma ba dole ba ce. Tana dai kara mata crispness

8- Sai ki kawo spices wanda kike so su ma ki zuba a kan flour din

9- Ki barbada curry shi ma ba dole ba ne amma yana sanya masa colour mai kyau da kamshi
10- Ki samu ziplock ko kuma container mai murfi. Ki tsame naman a ciki

11- Sai ki kawo wannan hadin na flour ki zuba a ciki

12- Ki jijjiga sosai don su garwaye

13- Ki dora mai a wuta ki yanka masa albasa sai ki kawo wannan nama ki soya da wuta medium low flame

14- Ki soya shi desired colour. Ni dai na fi so a golden brown
15- Then a tsame a yi serving shi ke nan

Idan kina son suya mai kyau, ki nemi non stick pan, akwai su kyawawa a Bakandamiya Shopping. Da sauran nau’ukan kayan kitchen masu kyau da kayatarwa.