Akwai hanyoyi da dama na sarrafa shinkafa. A yau na kawo maku wata mai sauki mai dadi, wadda kina cin ta tamkar kina cin kaza ne.
Abubuwan bukata:
1- 1 whole chicken
2- 3 cups rice
3- 1/2 teaspoon garlic paste
4- 2 onions
5- 2 tablespoons maggi and Mr Chef powder
6- 1 teaspoon salt
7- 1 sachet tomato paste
8- 1 sachet pepper and onion paste
9- 10 attarugu
10- 3 tomatoes
11- 2 tattasai
12- 1 and 1/2 cups oil
13- 1/2 teaspoon mixed spices
14- Mr Chef and maggi chicken flavors (1 sachet each) ko dai wani chicken seasoning din da kike da shi.
15- 6-8 seasoning cubes
For salad
1- 1/2 cucumber
2- 2 tomatoes
3- 1/2 onion
4- 2 boiled eggs
5- 1/2 teaspoon dakakken barkono
6- 1 teaspoon oil
Yadda ake yi:
1- Ki wanke kaza ki zuba albasa, garlic paste, seasoning and salt

2- Sai ki zuba ruwa, ki dora a kan wuta ki bari ta yi kamar minti goma zuwa sha biyar.

3- sai ki zuba kayan miyan da kika gyara kika wanke. Ki zuba mai, curry, da ruwa kadan.

4- ki zuba mixed spices sannan ki bari ya dahu har sai ruwan ya tsotse. Sai ki jajjaga su.
5- Ki zuba mai a cikin kyakkyawar tower pots dinki. Sai ki zuba garlic paste da albasa, tomato paste, da pepper and onion ki soya. Daga nan sai ki kawo wannan kayan miyan da kika jajjaga amma ba duka ba. Kamar rabinsu. Ki zuba. Sai chicken seasoning

6- Sai ki zuba ruwan nan da kika tafasa kaza da shi. Idan ba zai isa ki dafa shinkafar ba sai ki kara kadan. Ki zuba seasoning cubes

7- Sai ki dauko ragowar kayan miya ki zuba mai, dakakken barkono, da kuma dandano. Ki motse da kyau sannan ki shafa a kan kazar nan da kika tafasa.

8- Sai ki dauko kazar ki gasa a oven ko a gawayi.

9- idan ruwan ya tafasa ki zuba shinkafarki da kika wanke.

10- ki hada dark soy sauce da mai da yaji kadan ki dinga brushing a saman kazar. Kina yi kina juyawa har sai ta gasu na minti sha biyar zuwa ashirin.

11- Wannan kuma cucumber, tumatur, albasa, boiled egg, sai mai da yaji kadan na hada su na motse.

12- Sai ki serving a kyakkyawan cheffing dish dinki irin na Bakandamiya shopping
