Wannan wata kaza ce mai shape din butterfly. Tana da ban sha’awa a ido, sannan tana da matukar dadi. Idan aka ce peri peri kada ku dauka farfesu ake nufi, wani salon gashin kaza ne mai matukar dadi wanda kasashen ketare ne suka fi yin shi.
Abubuwan bukata:
1- 1 whole chicken
2- 1 cup peri-peri sauce
3- 1 tablespoon maggi powder
4- 1 teaspoon salt
5- 1 tablespoon spices
6- 1/4 cup oil
7- 1 tablespoon Oyester sauce
8- 1 tablespoon soy sauce
Yadda ake yi:
1- Ki zuba peri peri sauce a cikin bowl (tattasai, tarugu, shambo, albasa, ginger and garlic, oil, salt. Su za ki yi toasting sai ki markada a blender shi ke nan kin hada sauce din). Sai ki zuba seasoning da spices na yi amfani da paprika, black pepper, rosemary.

2- Sai ki zuba mai a ciki

3- Sai ki motsa da kyau su hade.
4- Sai ki nemi kazarki a bankara ta ta baya ba ta gaba ba. Ki wanke sosai da lemon tsami ko vinegar. Ki shafe ta tas da wannan hadin da kika yi. A kan baking tray

5- ki tabbata ta hade ko ‘ina har cikin kazar.

6- Ki zuba sauces din nan amma ba dole ba ne suna dai kara mata dandano da kamshi mai dadi.

7- Daga nan sai ki kai oven ki gasa ko kuma ki gasa a kan gawayi na minti arba’in zuwa awa daya. Idan kuma kazar Hausa ce sai ta kai awa daya da rabi saboda ta fi tauri.

8- Shi ke nan an gama sai a yi serving.
