Farfesu kala-kala ne, kuma akwai hanyoyi da yawa na sarrafa shi. A yau na zabi in kawo muku yadda ake yin farfesun naman sa da dankalin Turawa. Yana da dadi sannan yana da saukin yi. Dattawa da yara duk za su ji dadinsa musamman idan an bari ya dahu tubus.
Abubuwan bukata:
1- 1/2kg beef
2- 10 Irish potatoes
3- 3 attarugu
4- 1 tattasai
5- 1 albasa
6- 1 tablespoon seasoning
7- 1 tablespoon mixed spices
8- 1/4 cup vegetable oil
9- 2 cups water
Yadda ake yi:
1- Ki wanke naman tas sannan ki yanka shi shredded wato sirara dogaye

2- Sai ki zuba albasa da dandano
3- Ki zuba spices din da kike so. Na yi amfani da bay leaf, black pepper, paprika, thyme and rosemary.

4- Ki zuba mai a ciki

5- Ki jujjuya da kyau su hade. Amma ba za ki zuba ruwa ba.

6- Sai ki rufe ki bari da kansa zai fitar da ruwa.

7- Ga shi nan ba tare da na kara ruwa ko kadan ba amma ya fito. Hakan wata hikima ce da ke sanya nama ya yi zaki sosai.
8- Sai ki wanke dankali ki yanka shi daidai girman da kike so ki zuba a cikin naman

9- Ki kawo jajjagen tarugu da tattasai da albasa ki zuba a ciki.
10- Daga nan sai ki motsa

11- Sai ki zuba ruwa ba wani mai yawa sosai ba saboda already namanki ya dauko hanyar dahuwa.

12- Idan ruwan ciki ya ragu sannan kin tabbatar dankalin da naman sun yi taushi alamun sun dahu ke nan.
13- Ga shi nan bayan ya dahu sai ki sauke.

14- Shi ke nan an gama. Sai ki yi serving a kyakkyawan dinner set ko kuma soup bowls.

Idan kina neman kyawawan kitchen utensils tun daga kan su dinner sets, plates and bowls, blenders da sauransu, ku leka shafin Bakandamiya Shopping za ku samu komai.