Skip to content

Barbecue chicken wings

Share
barbecue chicken wings 1
1
(1)
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Da damar mutane ba su son cin fiffiken kaza musamman idan aka soya. Sai dai ba su sani ba akwai hanyar da za a bi a sarrafa shi ya kayatu ba fiye da tunaninsu. Watakila su cinye ba tare da sun gane me suka ci ba. Ku biyo ni domin ganin yadda ake yin barbecue chicken wings din nan.

Abubuwan bukata:

1- Fiffiken kaza guda hudu

2- 1 tablespoon multipurpose marinade

3- 2 cups vegetable oil

4- 1 tablespoon chili flakes

5- 1 teaspoon ketchup

6- 1 teaspoon barbecue sauce

7- 1 teaspoon light soy sauce

8- 1 teaspoon Oyester sauce

9- 1 teaspoon honey (or brown sugar)

10- 1 tablespoon butter

Yadda ake yi:

1- Na yi marinating fiffiken kaza da multipurpose marinade, na ajiye shi tsawon awa uku ya tsumu sosai sannan na dauko shi. Na dora mai a pan bayan ya yi zafi na zuba a ciki na soya da wuta kadan saboda kazar ta soyu sosai

barbecue chicken wings 1

2- Ga shi nan bayan ya soyu. Idan kika cika wuta zai zo cikinsa bai nuna ba

barbecue chicken wings 2

3- Sai ki kwashe mai. Ki zuba butter, idan ya narke sai ki zuba zuma (ko kuma brown sugar). Sai ki hada sauces (ketchup, oyester sauce, barbecue sauce, light soy sauce) duk ki zuba a ciki

barbecue chicken wings 3

4- Sai ki kawo chili flakes ki zuba ki jujjuya sosai

barbecue chicken wings 4

5- Daga nan sai ki dauko soyayyen wings din nan ki zuba a ciki ki motsa su hade sosai

barbecue chicken wings 5

6- Idan ya gama hadewa sai ki kwashe ki yi arranging a baking tray ki dan kara barbada chili flakes idan kina son extra pepper, sai ki saka a oven ki gasa na minti bakwai zuwa goma.

barbecue chicken wings 6

7- sai ki ciro shi daga oven a yi serving

barbecue chicken wings 7

How many stars will you give this recipe?

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page