Hadin awara da hanta abinci ne mai tasiri wajen gina jiki. Da farko dai ita awara ana yin ta ne da waken suya, saboda haka ta na daga cikin muhimman abinci masu gina jiki, wato protein. Ita ma hanta na daga cikin abinci mai samar da protein ga jiki. Don haka, wannan recipe, bayan kasancewar za a iya hada shi da kudi kalilan, yana da dadi da kuma alfanu ga lafiyar jiki na yaro da babba.
A tarihance, awara an kirkire ta ne daga birnin Sin (China) inda suke kiran ta da TOFU. Daga nan kuma ta rarrabu a sassan duniya da suna daban-daban. Ku biyo ni do ganin yadda ake wannan abinci mai dadi cikin sauki.
Abubuwan hadawa
- 20 pieces medium sized awara
- 1/4kg liver (hanta)
- 1 sachet tomato paste
- 1 cup pepper mix (tattasai and attarugu)
- 1 tablespoon spices of choice (Na yi amfani da black pepper, ginger and garlic powder, paprika, and curry powder. Duka na hade su ya ba ni 1 tablespoon).
- 3 maggi seasoning cubes plus 1/2 teaspoon onga powder (optional)
- pinch of salt
- 1 teaspoon of sugar (optional)
- Vegetable oil 35cl

Yadda ake hadawa
1. Ki zuba mai a cikin non stick work pan ki bar shi ya yi zafi.
2. Idan ya yi zafi sai ki zuba awara (A haka na saye ta wurin masu sayarwa. Nan gaba kadan zan kawo yadda ake dafa asalin awarar)

3. kada ki cika wuta don kada ta kone. Ki bari a hankali ta soyu.
4. Idan dayan gefen ya soyu sai ki juya dayan.
5. Ga shi nan bayan na juya.
6. Idan dayan gefen shi ma ya soyu sai ki kwashe.

7. Ki rage mai ya zama kadan (kamar 2-3 tablespoons). Sai ki zuba hanta wadda kika ya yanka ta into cubes kika wanke da kyau. (Ba a raba hanta da jini).

8. Ki zuba wannan kayan dandano da kayan kamshi, sai gishiri da sugar kadan (amma sugar ba dole ba ne, yana dai kara mata dandano mai dadi).

9. Sai ki jujjuya su a hankali su game duka. Ki bar su su dan soyu na akalla minti biyar.
10. Sai ki zuba biyu bisa ukun albasa mai lawashi (2/3)
11. Ki zuba tumaturinki.

12. Ki soya tumaturin na kamar minti daya.
13. sai ki zuba pepper mix din

14. Ki bari su soyu za ki ji kamshi yana tahi.
15. Sai ki zuba wannan soyayyar awara taki.

16. Daga nan sai ki rage wuta, ki jujjuya a hankali.
17. Sai ki juye ragowar lawashin albasa.

18. Ki yi serving a cikin kyakkyawan plate tare da cabbage da sauran vegetables din da kike so.

Za ku iya samun kyawawan plates da sauran nau’ukan kayan kitchen a Bakandamiya Shopping.