Na sha kawo maku hanyoyin sarrafa kaza, amma wannan kazar ta sha bamban da sauran. Kaza ce wadda kina cin ta tamkar kina cikin restaurants din Larabawa. Tun daga kan kamshinta har zuwa dandanonta abin so ne.
Abubuwan bukata:
1- 1 chicken
2- 1/2 teaspoon black
Pepper
3- 5 pieces cloves
4- 2 cinnamon sticks
5- 5 pieces green cardamom
6- 4 attarugu
7- 1 onion
8- 1 sachet chicken seasoning
9- 1/2 Sachet tomato paste
10- 1/2 teaspoon soy sauce
11 2 tablespoons oil
12- 4 seasoning cubes (2 maggi, 1 mr chef, and 1 terra)
13- 1 teaspoon salt
14- 1 tablespoon dakakken yaji (idan kina so).
Yadda ake yi:
1- ki raba kazar gida biyu ki wanke ta sosai sai ki saka a pan. Sai ki zuba attarugu wanda ba ki jajjaga ba da dandano

2- ki zuba gishiri. ki zuba spices din da na lissafa duka (sai kin dan soya su sama-sama sannan ki daka su zama gari. Ki diba ki zuba a kan kazar)
3- sai ki zuba albasa ki zuba ruwa ba mai yawa ba. Ki dora a wuta ki bari ta yi half done.

4- ki samu bowl, ki zuba ragowar spices din nan da kika daka. Then ki tsame attarugun da kika saka a naman ki jajjaga su ki juye a ciki.

5- Ki zuba dakakken yaji amma ba dole ba ne. Sai magi.

6- Ki zuba soy sauce

7- Sai tomato paste

8- Chicken seasoning ba dole sai irin wannan ba.

9- sai ki tsame kazar daga cikin ruwa. Ki motsa wannan hadin da kika yi.

10- ki zuba a kan kazar ki murtsuka da kyau su shiga cikinta.

11-ki dora a kan wuta ki gasa. Ki dinga yi kina juyawa kuma kada wutar ta yi yawa.

12- Ga ta nan bayan ta gama gasuwa. Sai ki sauke a yi serving.

– Za ki iya gasawa a oven, grill pan, ko dai duk abin da kike da shi. Akwai kayan gashi kala-kala a Bakandamiya shopping.