Hausawa suka ce ‘Alkaki sai a gidan sarauta’ ni kuma na ce a’a, ke da kanki sarauniyar kanki ce, kuma gidanki masarauta ce. A yau na kawo maku yadda za ku tsantsara alkakinku ta hanya mafi sauki.
Abubuwan bukata:
1- 1 mudu alkama
2- 1 sachet butter
3- 1/2 cup tsamiya
4- ruwa kadan
5- gwangwani uku mai
6- Gwangwani biyu sugar
7- 2 tsamiya
8- Ruwan kanwa 2 spoons
Yadda ake yi:
1- Ki gyara alkama ki barza ta

2- Sai ki zuba butter ki murza shi sannan ki zuba ruwan tsamiya. Ki kara ruwa kadan ki motsa sannan ki rufe ki bar shi a bokiti sai ya kwana a haka.

3- Ga shi nan bayan ya kwana. Za ku juye a cikin turmi ki zuba ruwan kanwa kadan ki yi ta dakawa. Ki dan zuba mai saboda kar ya like.

4- Ga shi nan bayan ya daku haka ake son shi. Yadda idan kin ja shi zai tafi alamun ya bugu da kyau ke nan. Za ki iya amfani da mixer babba ma.

5- Sai ki nannada shi kamar haka. Idan kin nada kamar igiya za ki dauko gefe da gefen ne ki manne su.

6- Daga haka sai ki ajiye shi na minti goma zuwa sha biyar

7- Sai ki dora mai a wuta ki soya shi golden brown

8- Ki samu tukunya ki zuba sugar da ruwa kadan ki jefa tsamiya. Sai ki bar shi ya dahu har sai ya fara danko. Sannan ki jefa alkakin a ciki ki motse da kyau. Ki bar shi ya tsumama a cikin ruwan sugan

9- Bayan kamar awa shida ko kuma ki bar shi ya kwana sannan a ci.
