Wannan tuwon madara ne mai kyau da tsari. Bai da wahalar yi kuma yana da dadi sosai. Yana da dadi a yi kyauta da shi musamman ga kananan yara. Sannan za a iya fara kasuwanci ma da shi.
Abubuwan bukata:
1- 1/3 cup water
2- 1/3 cup sugar
3- 1/2 teaspoon flavor
4- 2 cups milk
5- drop of pink color
6- 1 teaspoon strawberry flavor
Yadda ake yi:
1- ki zuba sugar da ruwa a pan ki bari su dahu har sai sugar ya gama narkewa duka. Sai ki zuba flavor ki motsa ya dan fara danko sannan ki kashe wuta. Ki zuba madara ki tuka.

2- sai ki raba shi biyu ki zuba food colour da strawberry flavor a guda ki motse da kyau har sai ya game sosai

3- Sai ki dauko cutter dinki ta tuwon madara, ki dibi pink kadan ki zuba a ciki ki danna shi da kyau. Sannan ki dora a kan wancan white da kikai flattening. Sai ki ciro shi.

4- za ki gan shi ya zama kamar haka

5- ki bar shi ya sha iska da kyau

6- Sannan ki packaging.
